Abdulmalik Nuhu

Abdulmalik Nuhu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abdulmalik Nuhu, Grocers, BY PASS, Gusau.

AREWA MUNYI ABIN KUNYAKamar yadda na wallafa labarin jiya, yau kwana hudu kenan, wadannan mata Árnà s**a sace yaran Musu...
03/05/2024

AREWA MUNYI ABIN KUNYA

Kamar yadda na wallafa labarin jiya, yau kwana hudu kenan, wadannan mata Árnà s**a sace yaran Musulmi daga jihar Sokoto s**a kai Abuja aka kamasu

Mutanen Arewa basu damu da yada labarin ba, abinda aka damu dashi yake trending shine labarin wata yarinya mai tallen zogale da aka yiwa waka

Mu sani cewa illar da wadannan Árná suke mana yafi wanda 'yan táadda ke yi, su 'yan ta'àdda idan sun kà$he Musulmi ya mutu da imani Aljannah zai tafi Insha Allah

Su kuma wadannan Àrna da suke satar yaran Musulmi zuwa suke su canza musu addini, wanda ya mutu ba addini $akamakonsa wúta, kunga anan illarsu yafi na 'yan táadda

Kamata yayi ace labarin nan shine yake trending amma abin haushi da takaici labarin wata yarinya mai zogale da aka yiwa waka shine yake trending a Arewa

Wannan zai nuna maka cewa an cinye Arewa da yaki, babu wani abinda ya rage a Arewa sai iskanci da sharholiyar banza da wofi, shiyasa zamu cigaba da ganin wulakanci, za'a cigaba da takamu yadda aka ga dama

Wannan da ace Musulmi ne s**a saci yaran Àrna na tabbata da duniya gaba daya sai ta girgiza da labarin

Ku duba ku gani fa, cikin wanda s**a sace har da jaririya 'yar sati biyu da haihuwa, abune mai ban tausayi, amma har a cikin manyan Malamai masu fada aji babu wanda ya fito yayi magana saboda tsoro da kwadayin rayuwar duniya

Arewa kam babu, an gama cinyemu da yaki

Allah Ya sauwake
~Datti Assalafiy

17/12/2023

DA YAWA DAGA CIKIN SU, SUN ZABI GOYON BAYAN BARAYI 'YAN BINDIGA FIYE DA JAMI'AN TSARON MU.

Sun yi fatan ace an kashe fararen hula a karamar hukumar Zurmi domin su bi suna yada gawarwakin al'umma, sai gashi gawarwakin barayi ne ake cigaba da tsintowa a cikin dazuzzuka da jami'an tsaronmu s**a bisu suna karkashewa.

Idan baku manta ba, a cikin satin nan hedikwatar tsaro ta Najeriya ta hannun mai magana da yawunsu, s**a fitar da sanarwa ta kididdiga da nasarorin da s**a samu akan maboyar ‘yan bindiga a yankunan Zamfara da Sokoto.

Haka kuma, Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Buba Edward, ya tabbatar da kashe kwamandojin ‘yan bindiga (4) a wani harin da s**a kai kwanan nan inda s**a kashe manyan 'yan bindiga kamar su:

1) Dan Muhammadu
2) Machika
3) Haro
4) Ali Alhaji Alheri wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje da sauransu.

Manya-manyan kwamandojin 'yan bindiga (21) ne jami'an tsaro s**a yi nasarar hallakawa a cikin wannan 'dan lokaci a hare-haren da suke cigaba da kai wa ta sararin samaniya a Zamfara, ga su kamar haka:

1) Kachalla Jafaru
2) Kachalla Barume
3) Kachalla Shehu
4) Tsoho
5) Kachalla Yellow Mai Buhu
6) Yellow Sirajo
7) Kachalla Dan Muhammadu
8) Kachalla Makasko
9) Sanda
10) Abdulbasiru Ibrahim
11) Mai Wagumbe
12) Kachalla Begu
13) Kwalfa
14) Ma'aikaci
15) Yellow Hassan
16) Umaru Na Bugala
17) Isyaka Gwarnon Daji
18) Iliya Babban Kashi
19) Auta Dan Mai Jan Ido
20) Yahaya Dan Shama
21) Kachalla Ali Kawaje, Shugaban ‘yan bindiga da ya kitsa sace daliban jami’ar tarayya ta Gusau.

An kuma samu nasarar kawar da 'yan bindiga a wurare daban-daban da s**a hada da Danjibga, dajin ‘Yar tsakuwa, Dajin Munhaye, Dajin Kauran Zomo, Dajin Dansadau, da kauyen Akuzo.

Ana samun gagarumar nasara a yakin da ake yi da ‘yan bindiga a Zamfara, Godiya ga Sojoji, shuwagabanninmu da kuma babban yabo ga wadanda ke bayan fage suna ba da tallafi da bayanan da ake bukata wanda ke kaimu ga cin nasara.

A tarihi ta'addanci a Zamfara, ba’a taba samun nasarar kashe manyan barayi marasa imani ba irin wannan lokacin.

Insha Allahu idan aka cigaba da addu'a, za’a samu sauki sosai a Zamfara, Zamfara zata zauna lafiya insha Allahu.

Allah ya ci gaba da tsare mana jami'an tsaron mu a fagen daga, Allah ka bamu dawwamammen zama lafiya, Allah ka taimaki shuwagabannimu. AMIN.

By Abdul Balarabe

11/12/2023

مساحكم السعيد
🛌

06/10/2023

Address

BY PASS
Gusau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdulmalik Nuhu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category