03/11/2026
SANARWA!
UMARNI GA DARAKTocin JIHOHI KAN BUƊE OFISHIN MEDIA OFFICER A DUKKAN MATAKAN AIKI
Babban Daraktan Agaji na Ƙasa, Sheikh Engr. Mustapha Imam Sitti, ya umarci Daraktocin Agaji na Jihohi da su gaggauta buɗe sabon ofishin da Majalisar Ƙasa ta amince da shi, mai suna Media Officer, domin amfani da wannan dama wajen inganta ayyukan agaji, yaɗa manufofin ƙungiya da kuma yaƙi da haramtattun ayyukan agaji a kafafen sadarwa na zamani.
Daraktan ya kuma bayar da umarnin cewa a buɗe wannan ofishi a dukkan matakan gudanarwa, wato State, Division, Detachment da Unit, domin tabbatar da ingantaccen tsarin aiki da sa ido kan harkokin yaɗa labarai da ayyukan agaji a kowane mataki.
GA TSARIN MUKAMAN DA AKA AMINCE DA SU:
1. STATE LEVEL
- State Media Officer
- Deputy State Media Officer
- Assistant State Media Officer
2. DIVISIONAL LEVEL
- Divisional Media Officer
- Deputy Divisional Media Officer
- Assistant Divisional Media Officer
3. DETACHMENT LEVEL
- Detachment Media Officer
- Deputy Detachment Media Officer
- Assistant Detachment Media Officer
4. UNIT LEVEL
- Unit Media Officer
- Deputy Unit Media Officer
- Assistant Unit Media Officer
Saboda haka, ana buƙatar dukkan Daraktocin Jihohi da su ɗauki wannan umarni da muhimmanci, tare da gaggauta aiwatar da shi a matakan da s**a dace.
Wannan tsari zai taimaka matuƙa wajen inganta sadarwa, bunƙasa ayyukan agaji, ƙarfafa sahihancin bayanai da kuma kare martabar ayyukan ƙungiya a kafafen sadarwa na zamani.
Allah Ya ba mu ikon sauke nauyin da ke kanmu cikin nasara. Amin.
Sanarwa: Ibrahim Baba Suleiman
(National Media Officer)
Jibwis Nigeria
03/11/2026.