16/04/2024
Idan Yahudawa Sukace Suna Tsoron Musulmai Toh Wadannan Suke Nufi!
1- Imam Rohollah Khomaini : Gwarzon namijin da ya samar da daular Musulunci guda daya wacce take qalubalantar mafi karfi da tasirin kasashen da yau suke juya duniya amma kasar Iran ta zame musu qadangaren bakin tulu, kasa daya tilo data dogara da kanta kuma take iya nuna yatsa ga kafircin duniya ta kwana lafiya!
2- Sayyid Aliyul Khamne'i : Tsohon soja kuma dakakkken namijin da ya zamewa yahudawa ala qaqai domin ci gaba daga inda Imam Khomaini ya tsaya, shekaru sama da arba'in da juyin Musulunci a Iran makiya suna ya aiki tukuru ba dare ba rana domin durkusar da wannan jaririyar daula ta Imam Mahdi amma Allah bai basu iko ba albarkacin tsayuwarsa da kuma tsantsan sallamawar sa ga fikirar mu'assasin daular, Imamur -Rahil Khomaini.
3- Sayyid Hassan Nasrullah: Cikakken jarumi mara tsoro da ya sakawa yahudawa yanke fata na cewar zasu mallaki qasar Lebanon da makwabtan ta ta hanyar yin fito na fito da haramtacciyar kasar israila da muzanta ta a idon duniya, da koya mata darasin da har yau idan yayi magana basa daukan ta da wasa. Sun san cewa shi sunan sa a fada a cika!
4- Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) : Sharifi jinin sayyida zahrah da Imam Ali kuma bakin fatar da ya tsayu da gwagwarmayar tabbatar da addini a nahiyar Africa da kuma koren duk wasu azzalumai masu yin babakere da dukiyar nahiyar ta hanyar tona asirin su da kuma wa'azozi da lekcocin da jinsu yake saka wa baqaqen fata cewa lalle akwai "hope" din cewa wata rana zasu fita daga kangin danniya da zalunci da yan' mulkin mallaka s**a jefa su na tsawan karnuka!
Idan kaji sunce suna tsoron musulmai kada ka dada kada ka rage kaga wadanda sukejin tsoro, domin su kadai ne s**a gano lagon su da manufarsu akan musulmi kuma suke aiki baji ba gani wajen tona asirin su!
Wadannan sune turakun gwagwarmaya, Allah ya kara musu lafiya, ya lullube Shugaban su Imam Khomaini da rahama mayalwaciya.