05/06/2026
HON. SANI IBRAHIM TANKO YA HALARCI MUHIMMIN TARON DA YA SHAFI GYARAN DOKAR SAYE DA KWANGILAR GWAMNATI A ABUJA
A YAU, MATAIMAKIN SHUGABAN KWAMITIN MAJALISAR WAKILAI KAN HARKOKIN SAYE DA KWANGILAR GWAMNATI (DEPUTY CHAIRMAN, HOUSE COMMITTEE ON PUBLIC PROCUREMENT), HON. SANI IBRAHIM TANKO, YA HALARCI WANI MUHIMMIN TARO NA YINI GUDA DA AKA GUDANAR A ABUJA KARKASHIN JAGORANCIN SHUGABAN KWAMITIN, DOMIN TATTAUNA BATUTUWAN DA S**A SHAFI AMFANI DA TSARIN SAYE DA KWANGILA TA HANYAR FASAHA TA ZAMANI (E-PROCUREMENT) DA KUMA GYARAN DOKAR PUBLIC PROCUREMENT ACT TA SHEKARAR 2007.
TARON YA MAYAR DA HANKALI KAN YADDA ZA A SAMAR DA INGANTACCEN TSARIN DOKA DA ZAI BA DA DAMAR AIKI DA FASAHA TA ZAMANI A HARKOKIN SAYE DA KWANGILAR GWAMNATI, TARE DA KARA GASKIYA, RIƘON AMANA, SAURIN AIKI DA KUMA TABBATAR DA AMFANI DA KUƊAƊEN JAMA'A YADDA YA KAMATA.
A MATSAYINSA NA MATAIMAKIN SHUGABAN KWAMITIN, HON. SANI IBRAHIM TANKO YA BA DA GUDUNMAWA MAI MUHIMMANCI A TATTAUNAWAR DA AKA GUDANAR, INDA AKA TATTAUNA HANYOYIN DA ZA SU TAIMAKA WAJEN GINA TSARIN DOKA NA ZAMANI WANDA ZAI TALLAFA WA AIWATAR DA E-PROCUREMENT A NAJERIYA.
WANNAN NA SAKE NUNA IRIN JAJIRCEWA, ƘWAREWA DA KUMA KISHIN KASA DA HON. SANI IBRAHIM TANKO KE NUNAWA WAJEN CIKA NAUYIN DA AL'UMMAR SHIRA/GIADE FEDERAL CONSTITUENCY S**A DORA MASA, TARE DA BA DA GUDUNMAWA GA TSARE-TSARE DA DOKOKIN DA ZA SU KAWO CIGABA MAI ƊOREWA GA KASA.
MUNA ALFAHARI DA WAKILCIN DA UBANGIDANMU HON. SANI IBRAHIM TANKO KE YI A MAJALISAR WAKILAI, INDA YAKE CIGABA DA ƊAGA MARTABAR MAZABAR SHIRA/GIADE DA JIHAR BAUCHI A IDON DUNIYA.
ALLAH YA ƘARA MASA LAFIYA, BASIRA, HIKIMA DA NASARA DOMIN CIGABA DA HIDIMTA WA AL'UMMARSA DA KASA BAKI ƊAYA.
/GIADE_DECIDED!
BABU GUDU, BABU JA DA BAYA! 💪🇳🇬🔥
✍️✍️
DSTB 😎💥📷