01/10/2025
DAGA KARAMAR HUKUMAR MULKI TA SURU
SEN ABUBAKAR ATIKU BAGUDU YA SAMARWA AL'UMMAR KARAMAR HUKUMAR MULKI TA SURU WUTAR SOLAR WADDA ZA TA AMFANI GIDAJE AƘALLA DUBU BIYU.
Mai girma Minista Sen. Abubakar Atiku Bagudu yayi nasarar samarwa al'ummar yankin Karamar hukumar Mulki ta Suru wutar solar mai aiki da hasken rana wadda za ta amfani gidaje akalla gida dubu biyu a bisaga damar da ya sa mu karkashin mulkin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
An samarda wutar ne a garuruwan Suru, Bakwui, Giro da Dakingari da dake Karamar Hukumar Suru ta hanyar Hybrid Solar Mini Power Grid ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Wannan tsarin lantarki na hasken rana, mai ƙarfin 400kWp da tsarin ajiya na 100kWh, zai tabbatar da samun wuta ba tare da yankewa ba, da rana da dare.
Haka kuma, an saka fitilun da za su haskaka tituna da gari masu aiki da hasken rana wato (Solar Traffic light) Domin ƙara tsaro da jindaɗin rayuwa, tare da bai wa mutane damar gudanar da harkokin kasuwanci ba dare ba rana, cikin aminci da tsaro.
Bugu da ƙari, aikin yana haɗe ne da tsarin samar manyan Bohol Bohol masu aiki ta hanyar hasken rana, domin samarda ruwa masu tsafta, bi ma'ana an samar musu wutar solar da za suyi amfani da ita cikin gidaje, an samar musu fitillun solar da za su haskaka gari da tituna, da karshe kuma an samar musu da ruwan sha.
Wadannan ayukkan alkhairi sun ƙara tabbatar mana da manufar Renewed Hope Agenda na kawo cigaba mai ɗorewa da sauyi na alkhairi a cikin al'umma, samarda tsaro da inganta rayuwar ‘yan Najeriya ƙarƙashin mulkin Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da goyon bayan Gwamnan Jihar Kebbi DrDr Nasir Idris Kauran Gwandu, da jajircewar Sen. Abubakar Atiku Bagudu, wanda kullum ke sanya bukatun al’ummarsa a zuciyarsa cikin harkokin cigaban ƙasa.