Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka

Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka, Grocers, Bauchi.

Shugabannin Gamayyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdallah Caps, sun kai ziyarar gi...
11/06/2026

Shugabannin Gamayyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdallah Caps, sun kai ziyarar girmamawa ga Hon. Dr. Yakubu Adamu, ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi na Jam’iyyar APM, domin taya shi murnar samun tikitin takara tare da bayyana cikakken goyon bayansu ga tafiyarsa ta siyasa.

A yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa sun yanke shawarar mara wa Hon. Dr. Yakubu Adamu baya ne sakamakon nagartarsa, jajircewarsa da kuma irin hangen nesan da yake da shi wajen kawo ci gaba ga jihar.

Shi ma da yake jawabi, Hon. Sulaiman Mohammed Bello ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi da ta cika alkawarin tallafin da ta yi wa ƙungiyar, yana mai bayyana cewa sun fara ganin alamun aiwatar da wannan alkawari, tare da fatan za a kammala shi cikin gaggawa.

A nasa martanin, Hon. Dr. Yakubu Adamu ya nuna matuƙar godiya ga shugabannin ƙungiyar bisa wannan ziyara da kuma irin goyon bayan da s**a nuna masa. Ya tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da aiki tukuru domin samar da ci gaba mai ɗorewa da bunƙasa tattalin arzikin Jihar Bauchi idan aka ba shi dama.

An kammala taron da addu'o'in neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba ga Jihar Bauchi da al'ummar Najeriya baki ɗaya.

Kungiyar Gamayyar ’Yan Kasuwa Ta Kasa reshen Jihar Bauchi, karkashin jagorancin shugabanta, Hon. Abdullah Caps, ta kai z...
03/06/2026

Kungiyar Gamayyar ’Yan Kasuwa Ta Kasa reshen Jihar Bauchi, karkashin jagorancin shugabanta, Hon. Abdullah Caps, ta kai ziyara ga sabon shugaban Jam’iyyar APM na Jihar Bauchi domin taya shi murnar samun nasarar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar cikin lumana da nasara.

A yayin ziyarar, shugabannin kungiyar sun yabawa sabon shugaban jam’iyyar bisa jagoranci da kokarin da yake yi wajen hada kan mambobin jam’iyyar da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ’ya’yanta.
Haka kuma, kungiyar ta jinjina wa Gwamnan Jihar Bauchi bisa irin alherin da yake yi wa ’yan kasuwa da kuma kokarin bunkasa harkokin kasuwanci a jihar. Sun yi kira da a ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su taimaka wajen inganta rayuwar ’yan kasuwa da al’umma baki daya a sabuwar gwamnati da ake sa ran kafuwa nan gaba, da yardar Allah.

Kungiyar ta kuma bayyana cikakken goyon bayanta ga tsarin da Jam’iyyar APM ke tafiyarwa a Jihar Bauchi, tare da nuna gamsuwa da salon shugabanci da manufofin jam’iyyar. Ta jaddada aniyarta ta ci gaba da hada kai da jam’iyyar domin ci gaban jihar da walwalar al’umma.

Gamaiyyar Ƙungiyar Haɗaɗɗun ‘Yan Kasuwa da Masu Sana’o’i ta Jihar Bauchi ta kafa kwamitoci uku domin tsara makomarta a s...
03/05/2026

Gamaiyyar Ƙungiyar Haɗaɗɗun ‘Yan Kasuwa da Masu Sana’o’i ta Jihar Bauchi ta kafa kwamitoci uku domin tsara makomarta a siyasance.

Ƙungiyar Amalgamated Traders and Artisans Association (ATAA), reshen Jihar Bauchi State, ta gudanar da wani muhimmin taro na musamman domin tattauna harkokin siyasa da kuma makomar ƙungiyar a nan gaba.

A yayin taron, ƙungiyar ta amince da kafa kwamitoci guda uku da za su wakilci shiyyoyin Bauchi South, Bauchi Central da Bauchi North, domin su fara tuntubar ƙananan ‘yan kasuwa da masu sana’o’i a faɗin jihar.

An bayyana cewa an bai wa kwamitocin wa’adin mako biyu domin su kammala tattara ra’ayoyi da shawarwari daga ƙananan ‘yan kasuwa, wanda hakan zai taimaka wajen bai wa ƙungiyar damar tsayar da matsaya kan alkiblar da za ta dosa a siyasance.

Haka kuma, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi da ta ƙara himma wajen tallafa wa ‘yan kasuwa, musamman ƙananan ‘yan kasuwa, ta hanyar samar musu da jarin kasuwanci da kuma inganta yanayin gudanar da sana’o’insu.

Ƙungiyar ta kuma roƙi gwamnatin jihar da ta samar wa waɗanda aka cire daga wuraren kasuwancinsu wasu gurare na daban domin ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin sauƙi da walwala.

A gefe guda, ƙungiyar ta yabawa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, bisa irin ayyukan ci gaba da yake gudanarwa a ɓangaren kasuwanci, musamman aikin gina sabuwar kasuwa da ake yi a hanyar Ibrahim Bako Bypass.

Ƙungiyar ta bayyana wannan aiki a matsayin babban ci gaba da zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da samar da ingantaccen yanayi ga ‘yan kasuwa.

Haka zalika, ƙungiyar ta yaba da sauran ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke gudanarwa a faɗin Bauchi, tare da jaddada cewa a shirye take ta ci gaba da bai wa gwamnati cikakken goyon baya domin tabbatar da cigaban jihar da walwalar al’umma.

Shugaban ƙungiyar, Abdallah Caps, ya jaddada kudirin ƙungiyar na haɗa kan ‘yan kasuwa da kare muradunsu, yana mai cewa haɗin kai da tsari ne za su taimaka wajen cimma manufofin ƙungiyar da inga

AN ROKI GWAMNAN JIHAR BAUCHI YA KAI DAUKI GA MAYANKAN BAUCHI (KWATA)_________Shugaban gamayyar ƙungiyoyin ‘yan kasuwa na...
23/04/2026

AN ROKI GWAMNAN JIHAR BAUCHI YA KAI DAUKI GA MAYANKAN BAUCHI (KWATA)
_________

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin ‘yan kasuwa na jihar Bauchi ya roƙi Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, da ya kai dauki ga mahautan Kwatan Bauchi tare da ɗaukar matakin sabunta wurin domin ya dace da tsarin zamani.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara ta gani da ido da ya kai Kwatan Bauchi, bayan shugabannin ƙungiyar mahauta sun ziyarce shi a ofishinsa inda s**a gabatar da koken su kan halin da kwatan ke ciki.

Daga bisani ne ya kai ziyara domin ganewa idon sa yadda wurin yake.Ya jaddada cewa Gwamnan Jihar Bauchi ya shahara wajen kawo sauyi da cigaba, yana mai cewa ya riga ya sauya fasalin wurare da dama a jihar cikin wa’adin mulkinsa.

Ya ƙara da cewa gwamnan ya inganta gidajen sarauta, ya gyara gidan gwamnati tare da mayar da shi na zamani, sannan ya inganta kasuwanni da hanyoyi, wanda hakan ya sa yawancin sassan jihar s**a samu sabon salo na cigaba.

A ƙarshe, ya bayyana cewa akwai kyakkyawan fata cewa gwamnatin jihar za ta duba koken mahautan tare da ɗaukar matakin da zai kawo sauƙi da cigaba a Kwatan Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci, da yardar Allah.

Sabbin shugabannin ‘yan kasuwar Dr. Sulaiman Adamu Market, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Alhasino Adam, sun kai ziyara ofi...
21/04/2026

Sabbin shugabannin ‘yan kasuwar Dr. Sulaiman Adamu Market, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Alhasino Adam, sun kai ziyara ofishin shugaban gamayyar ƙungiyoyin ‘yan kasuwa na Jihar Bauchi, Alhaji Abdullah Cap, domin nuna godiya ga irin ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

A yayin ziyarar, shugabannin sun kuma miƙa koke kan wasu ‘yan kasuwa da s**a rasa rumfunansu sakamakon aikin gina gadar sama (Flyover) a yankin Central Market. Sun bayyana cewa, duk da cewa an raba filayen diyya,

Amma su na daga cikin ‘yan kasuwar da abin ya shafa sai dai su baa haɗa su cikin waɗanda s**a amfana ba.

Nan take, shugaban gamayyar ƙungiyoyin ‘yan kasuwa, Alhaji Abdullah Cap, ya ɗauki matakin kai koken ga hukumomin da abin ya shafa, inda aka amince za a duba lamarin cikin gaggawa tare da tabbatar da ba su filayen diyya. Kamar yanda aka Baiwa yan Central Market

Haka kuma, an buƙaci shugabannin ƙungiyar su gabatar da cikakken jerin sunayen mambobinsu domin sauƙaƙa aiwatar da matakin.

Shugabannin ‘yan kasuwar sun bayyana jin daɗinsu da wannan mataki, tare da jaddada cikakken goyon bayansu ga gwamnatin jihar Bauchi, inda s**a yi alkawarin ci gaba da marawa gwamnati baya 100%, domin inganta harkokin kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arzikin jihar.

20/04/2026
Sabbin shugabannin ƙungiyar mahauta na ƙaramar hukumar Bauchi sun kai ziyara ofishin shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin ’Yan K...
20/04/2026

Sabbin shugabannin ƙungiyar mahauta na ƙaramar hukumar Bauchi sun kai ziyara ofishin shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin ’Yan Kasuwa na ƙasa reshen Jihar Bauchi, Alhaji Abdullah Cap.

A yayin ziyarar, shugabannin sun bayyana koke kan halin da kwatan Bauchi (wurin yanka nama) ke ciki, inda s**a ce akwai matsaloli da dama da ke buƙatar kulawar gaggawa daga gwamnati.

Sun buƙaci shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin ’Yan Kasuwa da ya kai ziyara zuwa kwatan domin ganin halin da ake ciki da idonsa, tare da isar da ƙorafinsu ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi.

Nan take, Alhaji Abdullah Cap ya amsa kiran nasu, inda ya ba su tabbacin cewa zai kai ziyarar gani da ido domin fahimtar matsalolin da kuma kai ƙorafinsu ga gwamnati domin a samo mafita.

‎‎Shugaban Hadakan Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu Ya Karɓi Baƙuncin Shugabannin Ƙungiyar Mahauta.‎‎A jiya Asabar ne, S...
19/04/2026


‎Shugaban Hadakan Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu Ya Karɓi Baƙuncin Shugabannin Ƙungiyar Mahauta.

‎A jiya Asabar ne, Shugaban Haɗakan Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu na Jihar Bauchi, Hon. Abdullah Caps, ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Mahauta na Ƙaramar Hukumar Bauchi a ofishinsa.

‎Ziyarar ta zo ne domin ƙara dankon zumunci da ƙarfafa alaƙar aiki tsakanin ɓangarorin biyu, tare da tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi ci gaban kasuwanci da sana’o’i a jihar.

‎A yayin ganawar, Hon. Abdullah Caps ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ‘yan kasuwa da masu sana’o’i, yana mai cewa hakan na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga al’umma.

‎Shugabannin Ƙungiyar Mahauta sun bayyana godiyarsu bisa kyakkyawar tarba da s**a samu, tare da nuna aniyarsu na ci gaba da bada gudummawa wajen cigaban harkokin kasuwanci a jihar Bauchi.

Shugaban Haɗaɗɗun Yan Kasuwa na Jiha Ya Mika Ta’aziyya ga Chairman Ƙananan Yan Kasuwa.‎‎Shugaban Haɗakan Yan Kasuwa da M...
05/04/2026

Shugaban Haɗaɗɗun Yan Kasuwa na Jiha Ya Mika Ta’aziyya ga Chairman Ƙananan Yan Kasuwa.

‎Shugaban Haɗakan Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu na Jihar Bauchi, Hon. Abdallah Caps, ya jagoranci tawagar ‘yan kasuwa zuwa ziyarar ta’aziyya ga Chairman Ƙananan ‘Yan Kasuwa, Alhaji Bala Roget, bisa rasuwar mahaifiyarsa.


‎A yayin ziyarar, Hon. Caps ya bayyana alhininsa da jimami bisa wannan babban rashi, yana mai addu’ar Allah Ya jikan mamaciyar da rahama, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya kuma ba iyalanta haƙurin jure wannan rashi.

‎Tawagar ta kuma jajanta wa iyalan mamaciyar tare da nuna goyon baya da tausayi a wannan lokaci na jimami.
‎Allah Ya jikanta da rahama, Amin.

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amalgamated Union Trader And Artisans Bauchi LGA Hadaka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category