Madubin Bauchi

Madubin Bauchi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Madubin Bauchi, Balganuhausa, Bauchi.

Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Murtala Asada, Ya bayyana cewa "Ban Ga Laifin Ķiristoçìn Nijer...
07/11/2025

Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Murtala Asada, Ya bayyana cewa "Ban Ga Laifin Ķiristoçìn Nijeriya Ba Don Sun Koka Cewa Ana Kaśhe Musù Mutanè Saboda Suna Kishin Na Su, Amma Manyan Arewa Har Karyatawa Suke Idan Muka Fito Muka Ce Ana Kashè Mutanè, Nan Wani Malami Ma YaJe Kebbi Ya Dawo Lafiya Bai Ga Matsalar Tsaro Ba, Cewar Sheik Murtala Assada

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UNTA’AZIYYA GA GWAMNAN JIHAR BAUCHI DA DUKKAN AL’UMMAR TOROHAJIYA ZAINAB NARABI ALLAH Y...
10/10/2025

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN
TA’AZIYYA GA GWAMNAN JIHAR BAUCHI DA DUKKAN AL’UMMAR TORO

HAJIYA ZAINAB NARABI ALLAH YA HASKAKA KABARIN KI.

Muna cikin alhini da jimami muna mika sakon ta’aziyya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Bauchi) tare da Gwamnatin Jihar Bauchi baki ɗaya, bisa rasuwar Sakatariyar Karamar Hukumar Toro, Hajiya Zainab Narabi.

Haka kuma, muna miƙa ta’aziyyar mu ga Mai Girma Ciyaman na Karamar Hukumar Toro, Pharm. Ibrahim Dembo Abubakar, bisa wannan babban rashi da ya shafi ofishin sa da al’ummar yankin gaba ɗaya.

Muna kuma jajanta wa daukacin al’ummar Narabi, mazauna Toro, da iyalan marigayiya bisa wannan babban rashi da ya tabbata a gare mu baki ɗaya.

Allah Madaukaki Sarki Ya gafarta mata, Ya karɓe ta cikin rahamarsa, Ya sa kabarinta ya zama dausayin Aljanna, Ya kuma ba iyalanta, Gwamnatin Jihar Bauchi, da daukacin jama’ar Toro haƙuri da juriya.

Hakika rashin Hajiya Zainab Narabi babban rashi ne, amma muna roƙon Allah Ya sa ta huta cikin aminci. Amin

KU JI RABO: Wata matashiya daga Gombe ta rubuta Alƙur’ani Mai Tsarki da hannuntaWata matashiya ‘yar Najeriya mai suna Fa...
06/10/2025

KU JI RABO: Wata matashiya daga Gombe ta rubuta Alƙur’ani Mai Tsarki da hannunta

Wata matashiya ‘yar Najeriya mai suna Fatama daga jihar Gombe ta kammala rubuta Alƙur’ani Mai Tsarki da hannunta gaba ɗaya, tun daga Fātiha har zuwa Nās, wato hizibi 60.

Rahotanni sun bayyana cewa Fatama ta ɗauki lokaci mai tsawo tana gudanar da aikin cikin tawali’u da niyyar neman lada daga Allah.

Shigo Shafin Jaridar 👉 Wakiliyar-Arewa 👈 Ta Nan, Ku Yi Following Yanzu Karku Bari Komai Ya Wuceku...

Gaskiyar Magana Tsantsa Daga Bakin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa"Kowacce ƙungiya, ko wacce Dariƙa ta je ta riƙe wawayenta...
02/10/2025

Gaskiyar Magana Tsantsa Daga Bakin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

"Kowacce ƙungiya, ko wacce Dariƙa ta je ta riƙe wawayenta, ta hana su magana, ko wacce ƙungiya ta duba waye sakarai yake taɓargaza bai da ilimi bai da basira bai da hikima bai da azanci yake yin son zuciya, ta hana shi wa'azi, ta hana shi riƙe makirfon, idan kowacce Dariƙa da kowacce ƙungiya ta yi haka to an samu matakin farko na gyara, dan wawayen su suke haɗa rigima." Inji Sheikh Daurawa

Me Zaku Iya cewa?

Dan Allah ku ringa taya mu da sharing zuwa groups...

Sanarwa domin samun ingantattun labarai kuyi following na:
Wakiliyar-Arewa
Madubin Bauchi
AGIBASA-Hausa

Wane Gwamna ne  salon Mulkinsa ya fi burgeku cikin Gwamnonin nan na Arewacin Nijeriya?. Ku bayyana mana ra'ayoyin ku.
24/09/2025

Wane Gwamna ne salon Mulkinsa ya fi burgeku cikin Gwamnonin nan na Arewacin Nijeriya?. Ku bayyana mana ra'ayoyin ku.

22/08/2025
Sarkin Musulmin Nijeriya Alhaji Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Rabi’ul Auwal ...
22/08/2025

Sarkin Musulmin Nijeriya Alhaji Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Rabi’ul Auwal 1447 a ranar Asabar, 23 ga watan Agusta 2025.

ALHAMDULILLAH NAKA SAI NAKA❤️Abinda Gwamnatin Tinubu ta gagara yi saboda banbancin da ake nuna mana 'yan Arewa, Maigirma...
07/08/2025

ALHAMDULILLAH NAKA SAI NAKA❤️

Abinda Gwamnatin Tinubu ta gagara yi saboda banbancin da ake nuna mana 'yan Arewa, Maigirma Jagoran siyasarmu a Nigeria Alhaji Atiku Abubakar ya dauki nauyin karatun 'yan matan Arewa wadanda s**ayi bajinta a gasar turanci na kasashen duniya da ya gudana a birnin London na Kasar England

Atiku zai dauki nauyin karatunsu har zuwa jami'ah a duk inda s**a ga daman yin karatun karkashin gidauniyarsa na Atiku Abubakar Foundation

Yaa Allah Ka cika wa Atiku Abubakar burinsa na alheri akan talakawan Nigeria 🙏

Ranar Friday akwai shan kallo Ashe da Kilishi da summayya ubansu dayane ita kilishi Yar tsintuwace. Akwai chakwakiya fak...
04/08/2025

Ranar Friday akwai shan kallo Ashe da Kilishi da summayya ubansu dayane ita kilishi Yar tsintuwace. Akwai chakwakiya fa

kuyi Like na AGIBASA-Hausa

DA DUMI-DUMI: Sheikh Sani Yahaya Jingir Ya Janye Kalamansa Tare Da Bada Hakuri Kan Kalaman Da Ya Yi Wa Mataimakin Sa She...
18/07/2025

DA DUMI-DUMI: Sheikh Sani Yahaya Jingir Ya Janye Kalamansa Tare Da Bada Hakuri Kan Kalaman Da Ya Yi Wa Mataimakin Sa Sheikh Yusuf Sambo, Na Ziyarar Da Peter Obi Ya Kawo Mishi.

Daga Muhammad Kwairi Waziri

16/07/2025

Akwai Darasi A Mutuwãr Buhari Wanda Sai Mai Haɲkali Ne Kaɗai Zai Gane, Cewar Dogonbauchi

Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa na gyara a Najeriya amma an fi ƙarfinsa. (Cabals) sun zagaye shi, azzalumai marasa gaskiya su s**a yi mulkin Najeriya".

Kwamishiniya a hukumar ƙidaya ta ƙasa reshen Jihar Kaduna, Hajiya Sa’adatu Garba Dogonbauchi, ta bayyana takaicinta kan yada wasu suke murna da mutuwar Buhari, a cewarta, "Na yi baƙin cikin yadda mutanenmu ƴan Arewa, Hausawa, musulmai ake ta kaɗe-kaɗe da murna, ko ma me Janar Muhammadu Buhari ya yi bai kamata a saka masa da irin wannan ba". In ji ta.

Dogonbauchi wadda ta bayyana haka ta cikin wata tattaunawarta da Dokin Ƙarfe TV, ta ci gaba da da cewa "Ku tuna cewa Janar Muhammadu Buhari bai satar muku kuɗi ba, ya mutu ba shi da Rijiyar mai, ya mutu gidansa ƙwaya biyu ne rak! Daga Daura sai Kaduna, har ya mutu ba shi da gida a Abuja. Janar Muhammadu Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa na gyara a Najeriya amma an fi ƙarfinsa. (Cabals) sun zagaye shi, azzalumai marasa gaskiya su s**a yi mulkin Najeriya". In ji ta.

A cewar Hajiya Sa’a, "Ya kamata mu sani ɗan’adam tara yake bai cika goma ba. Kuskuren Janar Buhari shi ne da ya ɗauki amana ya ba wa maciya amana saboda kullum suna zuwa masa da fuskar muminai. Ya so ya yi gyara a Najeriya amma maciya amana azzalumai sun bebaye shi. Ga yanayi na rashin lafiya da ya same shi". A cewarta.

Daga nan ta ci gaba da cewa, "Ina jan hankalin ƴan’uwa ƴan Arewa da ƴan Najeriya gaba ɗaya, da mu sani cewa inda Janar Muhammadu Buhari ya je duk ɗinmu za mu je". In ji Dogonbauchi.

Hajiya Sa’a, ta kuma yi kira ga muƙarraban gwamnatin Tinubu da su kiyaye masa amanar da ya ba su domin gudun irin abin da ya faru da Buhari a wannan lokaci. Haka kuma, ta ƙara da yin kira ga ƴan Najeriya da su zamto masu sanya shugabanni cikin addu’a.

Daga ƙarshe kuma, ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalai da ƴan’uwan marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari tare da fatan Allah Ya ji ƙansa Ya gafarta masa. "Buhari Uba ne kuma gwarzo ne da ya bar ɗumbin tarihi". A cewarta.

Me zaku iya cewa?

Dan Allah ku ringa taya mu da sharing zuwa groups.

Sanarwa domin samun ingantattun labarai kuyi following na
ALPU Hausa
AGIBASA-Hausa
ALIB Hausa
Madubin Bauchi
Madubin Arewa
Nigeria Hausa
Madubin-Arewa-TV
ANNUR-Hausa
Madubin Arewa TV
Wakiliyar-Arewa
BDC Hausa
Wakiliyata
AGIBASA-Hausa

Address

Balganuhausa
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madubin Bauchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share