TALBA TIGGI

TALBA TIGGI Ɗan tafiyar NNPP �
Masoyin Jagora Engr. Rabiu Musa Kwankwaso da Jakada Kabi. Muna tare don cigaban ƙa

🌟 BARKA DA SHIGOWA ADC 🌟Muna miƙa sakon taya murna da farin ciki gaMai Girma Jagora Engr. Abu Sadeeq Jakada Kabibisa shi...
11/04/2026

🌟 BARKA DA SHIGOWA ADC 🌟
Muna miƙa sakon taya murna da farin ciki ga
Mai Girma Jagora Engr. Abu Sadeeq Jakada Kabi
bisa shigowarsa cikin jam’iyyar ADC.
Wannan mataki da ka ɗauka alama ce ta jajircewa, hangen nesa, da kuma ƙudurin kawo cigaba mai ɗorewa ga al’ummar mu.
Al’ummar Kebbi ta Arewa na da cikakken yaƙini cewa zuwanka ADC zai ƙara ƙarfin gwiwa, haɗin kai, da kuma sabuwar fata ga siyasar yankinmu.
👉 Muna fatan wannan tafiya ta zama alheri
👉 Allah ya ba ka nasara a dukkan matakai
👉 Ya sa wannan sauyi ya zama mafita ga al’umma
Jagora, muna tare da kai a wannan sabuwar tafiya!
✍️ Daga magoya baya masu kishin cigaban Kebbi

🌙✨ SAKO NA BARKA DA SHAN RUWA ✨🌙Assalamu Alaikum Warahmatullah.Ina mika sakon Barka da Shan Ruwa ga daukacin al’ummar Mu...
08/03/2026

🌙✨ SAKO NA BARKA DA SHAN RUWA ✨🌙
Assalamu Alaikum Warahmatullah.
Ina mika sakon Barka da Shan Ruwa ga daukacin al’ummar Musulmi baki daya. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya amsa addu’o’inmu, Ya yafe mana kura-kuranmu.
Ya Allah Ka sa mu gama wannan azumi cikin koshin lafiya da imani mai karfi. Ka ba mu ikon ci gaba da ayyukan alheri bayan watan nan. 🤲
Barka da Shan Ruwa, Allah Ya maimaita mana da alkairi.


’a

SubjectSubjectMuna yi wa Mai Girma Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso da Jagora Engr Abu Sadeeq Jakada Kabi fatan alheri yayin...
05/02/2026

Subject
Subject
Muna yi wa Mai Girma Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso da Jagora Engr Abu Sadeeq Jakada Kabi fatan alheri yayin tafiyarsu zuwa ƙasar waje. Allah Ya tsare su, Ya ba su nasara a duk abin da s**a je nema, Ya dawo da su gida lafiya. Muna alfahari da jagorancinku da ƙoƙarin da kuke yi domin al’umma. Allah Ya ƙara ɗaukaka. 🤲

Muna yi wa Mai Girma Jagora Engr. Abu Sadeeq Jakada Kabi fatan alheri a ƙarshen wannan mako. Allah Ya saka da alheri bis...
25/01/2026

Muna yi wa Mai Girma Jagora Engr. Abu Sadeeq Jakada Kabi fatan alheri a ƙarshen wannan mako. Allah Ya saka da alheri bisa ƙoƙari da jajircewarka wajen hidima. Allah Ya ƙara maka lafiya, hikima da nasara, Ya kare ka da iyalanka, Ya cika mana buri da alkhairi. Amin

Ina mika godiya ta musamman da yabon zuciya zuwa ga Mai Girma Chairman NNPP Kebbi State, Hon. Musa Suleiman, bisa jagora...
31/12/2025

Ina mika godiya ta musamman da yabon zuciya zuwa ga Mai Girma Chairman NNPP Kebbi State, Hon. Musa Suleiman, bisa jagoranci nagari, kulawa da kuma irin goyon bayan da kake bai wa ‘ya’yan jam’iyya a kowane lokaci.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara maka lafiya, hikima da nasara a dukkan al’amuranka, Ya tsare ka da iyalanka, Ya kuma saka da alheri bisa duk abin da kake yi domin cigaban jam’iyya da al’umma.
Allah Ya ƙara ɗaukaka, Ya tabbatar da alherinka, Ya kuma ba ka ikon ci gaba da jagoranci cikin adalci da gaskiya. Ameen.

Kwankwasiyya ba hayaniya ba ce, tsari ce.Ba rikici ba ne, ladabi ne.Ba son rai ba ne, biyayya ce.Mu ‘yan Kwankwasiyya mu...
29/12/2025

Kwankwasiyya ba hayaniya ba ce, tsari ce.
Ba rikici ba ne, ladabi ne.
Ba son rai ba ne, biyayya ce.
Mu ‘yan Kwankwasiyya mun yarda da bin doka da oda,
mun yarda da tafiya bisa tsari da jagoranci nagari.
Muna tsayawa tsayin daka wajen biyayya ga tafarkin
Jagora Engr. Rabiu Musa Kwankwaso,
jagoran gaskiya, nagarta da ci gaban al’umma.
Duk inda Kwankwasiyya ta dosa,
can ne makomar adalci, zaman lafiya da cigaba.
Kwankwasiyya sai tsari.
Kwankwasiyya sai biyayya.
Kwankwasiyya sai Jagora.

“Ga mahasada da makiya masu fatan ganin bayan Jagora Engr. Abubakar Sadeeq Jakada Kabi, ku yi haƙuri ku juya ku kalli ba...
15/12/2025

“Ga mahasada da makiya masu fatan ganin bayan Jagora Engr. Abubakar Sadeeq Jakada Kabi, ku yi haƙuri ku juya ku kalli bayanku. Jagora bai tsaya don burge kowa ba; yana tafiya ne da gaskiya, adalci da amana. Yayin da kuke jira ya juya baya, shi kuma yana ci gaba da gaba, yana barin tarihi mai ɗorewa.”

Address

Gwazange Area
Argungu
861101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TALBA TIGGI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category