16/03/2026
UPDATE
1 Reshe ya juye da mujiya! A yayinda Mai fitowa ya sanar da mutuwar mutane, a yanzu ake tababar tasa mutuwar, wato Malam Bilya, inda a jiya ma wata ayar tambayar ta sake bulla bayan da majalisar Tuyan kasar ta yi zaman jawabinta amma babu Malam Bilya wanda aka saba shi ke bude taro ya rufe da addu'a. A wani kokari na karyata bidiyo me yatsu shida, wata barakar ta kara bulla inda aka ce ko da bidiyon malam din gaskiya ne a ciki, menene ya b***e masa hakorin gatsa na bangaren dama? Domin dai kowa ya san bakin Bilya cike yake da hakoransa farare cifcif kan a fara tuya.
2 Duk da an mayar da ofishin jakadancin Sufafawa na Makwabciyar Shahidai garwashi k**ar yadda a ka wa babban birnin Yahuza, bincike ya ce mutum biyu ne kawai wata yar leda ta taba su, kuma tuni aka share musu ita. Sai dai duk da haka Sufafawa tace su hada yanasu yanasu su bi ta sahara su bar yankin nan tunda su basa mutuwa gara a bar masu mutuwar yankin su ci gaba da diban maniyyata zuwa lahira, tuni dai al'ummar yankin ke kukan an ci amanar kauna da suke wa Sufafawa tunda ga shi tana ci gaba da barinsu a jangul don ta ceci shafaffu da mai
3 Shugaban Sufafawa na ci gaba da kiran abokansa da su taya shi wannan hidima, inda a yanzu haka yake bayyana kokon bararsa na ganawa da Danmatumburi me remote din tayar da duniya inda ake sa ran a ganawar Shugaban Sufafawa zai jaddada masa cewa duk fa tsiyarsa da takalar fadan da yake ba zasu tanka shi ba, don haka gara ma ya hakura
4 Wani Malamin Makaranta yayi ikirarin samar da sabon takanalojiyar koya wa yara gujewa mugayen hakaye goma shadaya a cikin kalma daya, hakayen wadanda s**a hada da karya, munafurci, yaudara, rashin ta ido, mugunta, son kai, neman yara kanana, Almubazzaranci, rashin bin doka, dakikanci, fariya kwadayi, malamin ya ce a yanzu maimakon tsawaita bayani akan kowane hali guda za a iya cure wannan halaye a kalma daya, wato Shugaban Sufafawa, idan aka cewa yaro kada yayi koyi da wannan mahaluki, to fa ya kubuta daga wadannan halaye 11
5 Jama'ar Sufafawa sun yi gangamin yin Allah Ya isa ga duk wanda ya dauki ko kwandalarsu ce ya sake saya wa wata tukubar suya hular kwano, taron Ala tsinen ya zo ne a daidai lokacinda kasar Shahidai ke cewa dama fa ita wani harin ba ta kai shi bane don ta toya kowa ba, sai don ta karar da hulunan kwanon sannan ta yi amfani da dutse daya tal wajen jefe tsuntsaye barkatai, da s**a hada yin amfani da Dubu ihirin kacal wajen kona Dala mulyan 300 ta yan bani na iya.
7 A wani gefen an ji kasar ta Shahidai na kidaya rijiyoyin man da s**a balaga s**a kai a jefa musu kuri'a muddin Shugaban Sufafawa ya jefa wa nasu kuri'a, tuni Shugaban Sufafawar ya fito ya ce shima bai ce zai kai kayan kuri'a can ba, don ya san hali, mutanen na iya jefa wata babbar kuri'a zuwa inda ake kawo masa kyautar dala tiriliyan guda a doron bayan rakuma.
8 An ce mayen Gwamna ya nada majalisar Sarki wadda ya ce zata taya shi ayyukan gudanar da mulki idan an karbo masa kasar Shahidai, duk da tuni iyayen gidansa s**a ce su fa sun janye batun sauya mulki a wannan kasa me taurin kai
Mu shakata da Hoton nadin halifan Rigiri