Almajirin Sayyid Ibraheem Zakzaky

Almajirin Sayyid Ibraheem Zakzaky Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Almajirin Sayyid Ibraheem Zakzaky, Grocers, aliyuibrahimmm33@gmail. com, Abuja.

'MUHIMMANCIN CIYAR DA MAI AZUMI..'__Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yace:"Manzon Allah yana  cewa; Yaku mutane wanda ya ciya...
20/02/2026

'MUHIMMANCIN CIYAR DA MAI AZUMI..'

__Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yace:

"Manzon Allah yana cewa; Yaku mutane wanda ya ciyar da mai azumi mumini a wannan wata, zai samu ladan 'yanta wuya wajen Allah, da kuma gafaran duk abun da ya shude na zunubansa. S**a tambaye shi, s**a ce; Ya rasulullah ba kowane yake iya ciyar da mai azumi ba ai. Yace, kuji tsoron wuta koda da rabin dabino ne.

Domin Allah ta'ala yana bada wannan lada mai yawa ga wanda ya yi aiki kadan, "Wato koda tsagin dabino ka bayar ko kuma kurbin ruwa in shi zaka iya, to shima zaka samu wannan ladan. Wato ma'ana ba sai kana da wadata zaka ciyar ba, 'dan Abin da kake da shi ma ka bayar aci. Yace, Yaku mutane wanda ya kyautata halinsa a wannan wata, to zai tsallake siradi rananda kafafuwa suke zamewa.

-Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Ja'afar Muhammad Jr.
©ZARIA MEDIA FUROM

Ga Fadawa a Gaban Mujaddadi.💥 💥 Ni Sanqira na ce: "Fadawa a gaban Jagoransu. An gaishe ku Fadawan Bawan Allah, Fadawan I...
02/08/2025

Ga Fadawa a Gaban Mujaddadi.
💥 💥
Ni Sanqira na ce: "Fadawa a gaban Jagoransu. An gaishe ku Fadawan Bawan Allah, Fadawan Ibrahewmul Magrib. Kun cika 'ya'ya na halas. Fadanci a gaban bawan Allah ya fi Fadanci a gaban Sarkin Gargajiya

An gama rufa-rufa yau an faɗi gaskiya. Tun watan jiya Zhul Hijjah kuma Yuni, Major-Jazzar ya shura. Inji Maulana Sheikh ...
14/07/2025

An gama rufa-rufa yau an faɗi gaskiya. Tun watan jiya Zhul Hijjah kuma Yuni, Major-Jazzar ya shura. Inji Maulana Sheikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky Hafizahullah.

Kuyi mana Sharing posting ɗin nan.

Ashura darasine babban gaske shiyasa kuma rayashi raya wannan addininne -syd zakzaky (h)
14/07/2025

Ashura darasine babban gaske shiyasa kuma rayashi raya wannan addininne

-syd zakzaky (h)

29/06/2025
29/06/2025

KARANTA DA HAKURI

Lokacin Da Yazid Ya Hau Karagar Mulki…

Bayan rasuwar Mu'awiyah, ɗansa Yazid ya hau karagar mulki a matsayin khalifa. Wannan lamari bai samu karɓuwa daga mutane da yawa ba, musamman daga fitattun sahabbai da zuriyar Annabi (S). Daya daga cikin wadanda s**a fi kiyayewa da mulkin Yazid shi ne Sayyid al-Shuhada, Imam Hussain (a.s).

Da zarar Yazid ya hau mulki, ya aika wasiƙu zuwa ga gwamnonin yankuna daban-daban yana umartarsu da su karɓo masa mubayi’ar mutane, musamman daga manyan mutane a Makka da Madina. Daga cikin waɗanda aka aike musu wasiƙa akwai gwamnan Madina a lokacin – wanda tarihun ya bayyana cewa shi ne al-Walid ibn Utbah ibn Abi Sufyan. A cikin wasiƙar, Yazid ya buƙaci gwamnan ya tilasta wa Imam Hussain da sauran fitattun mutane su yi masa mubayi'a, ko da da karfi ne.

Gwamnan Madina ya nemi shawara daga wani tsohon makaryaci kuma ɗan yaudara wanda tarihi ya fi sani da Mughira ibn Shu’ba. A nan ne wasu majiyoyi s**a nuna cewa ya bada shawarar a kira fitattun mutane su zo a daren, kafin labarin mutuwar Mu’awiyah ya bazu sosai. Aka aika kiran su Imam Hussain, Abdullahi ibn Umar, Abdullahi ibn Zubair, da sauransu.

Sai dai daga cikinsu, Imam Hussain (a.s) kadai ne ya amsa kiran da dare. Sauran sun ƙi zuwa. Imam Hussain ya nuna ladabi da dattaku, ya tafi, amma ya ƙi amincewa da mubayi'ar Yazid.

Lokacin da Imam Hussain ya isa fadar gwamna da dare, an karanta masa wasiƙar Yazid a bainin gwamnan da wani azzalumi mai suna Marwan ibn al-Hakam, wanda yana kusa da gwamnati a lokacin. Wasiƙar tana ɗauke da umarni kai tsaye daga Yazid cewa:

“Ka tilasta wa Hussain ya yi mubayi’a nan da nan. Idan ya ƙi – ka yanke kansa ka turo mini.”

Wannan umarni ne na kisa kai tsaye idan Imam Hussain bai yarda da mulkin Yazid ba.

Sai al-Walid, wanda ko da yake yana cikin gwamnati, bai son ya zubar da jinin dansa Fatima cikin gida ba. Ya so ya warware lamarin cikin salama, don gudun tashin hankali. Don haka, ya karanta wasiƙar ya kuma nemi Imam Hussain ya yi mubayi'a.

Imam Hussain (a.s) ya amsa da hikima kamar yadda addini ya koya, ya ce:

“Ina ganin lamarin ba zai warware a yanzu ba. Mubayi’a irin wannan ba a boye take ba. Bari a kira mutane, idan ka gayyace ni da jama’a na, zan bayyana matsayina.”

Wannan jawabi ya nuna cewa bai yarda a tilasta masa ba. Bai yarda da Yin mubayi'a da mutumin da bai cancanta ba.

Amma Marwan ibn al-Hakam ya murɗe fuska ya ce:

“Ka kashe shi yanzu! Wallahi, idan ya fita daga nan, ba zaka sake samun shi ba!”

Sai Imam Hussain ya kalle shi da karfin hali ya ce:

“Kai ne kake so a kashe ni? Wallahi, kai da Yazid za ku iya shiryawa da kansa.”

Al-Walid bai yarda a kasheshi cikin gida ba, don gudun tashin hankali. Imam Hussain (a.s) ya fita lafiya, yana tare da ‘yan'uwansa da mayakansa.

Daga nan ne Imam Hussain ya yanke shawarar barin Madina gaba ɗaya, saboda ya fahimci cewa idan ya zauna, za a yi masa kisa cikin sirri, ko kuma a tilasta masa mubayi’a ga mutumin da ya keta dokokin addini.

Wannan lamari yana nuna jarumta da hangen nesa na Imam Hussain (a.s), da rashin yarda da zalunci ko da kuwa zai fuskanci mutuwa. Wannan dalili ne yasa Shi'a da dama suke cewa:

“Karbala ta faro daga Madina.”

وَلَكِنْ لَا يَوْمَ كَيَوْمِكَ يَا أَبَا عَبْدِ اللَّهِ 😭😭

Assalamu Alaika Ya Aba Abdullahil Hussain (A.S)

29/06/2025

Kissa: Imam Ali da Yahudi da Babbakar Riga(kayan Yaqi)

A wata rana, Imam Ali (A.S) ya rasa babbakar rigarsa (wato kayan yaki ko tufafin daraja). Bayan kwanaki sai ya gan ta a hannun wani mutum kirista a kasuwa yana sayarwa.

Imam Ali ya tafi gaban alkali don ya shigar da kara. Ka tuna, shi ne shugaban Musulmi, kuma yana kai karar kirista!

Alkalin kuwa shi ne Shurayh, wanda ya san daidai matsayin Ali, amma ya tabbatar da gaskiya.

Sai Imam Ali ya ce:

“Wannan rigar tawa ce. Na rasa ta kwanaki baya. Na same ta a hannun wannan kirista.”

Alkalin ya tambayi kiristan:
“Kana da shaida cewa kai ne mallakin rigar?”

Kiristan ya ce:
“Eh, na saya a kasuwa kuma babu wanda ya zo da shaida akan ita.”

Shurayh ya dubi Imam Ali ya ce:
"Ya Amirul Mu’minin, baka da shaida?"

Imam Ali ya ce:
“A’a, amma na san tawa ce.”

Sai alkali ya yanke hukunci ga kiristan, domin gaskiya tana buƙatar shaida.

Kiristan ya yi mamaki ƙwarai, ya ce:
“Kai shugaban Musulmi ne, kuma ka zo kotu kamar kowa? Kuma alkali ya hukunta a kanka, ka karɓa ba da ƙorafi ba?”

Sai ya fashe da kuka, ya ce:

“Wannan gaskiya da adalcin ne s**a sa na karɓi Musulunci. Lallai wannan rigar tawa ce, amma na same ta a kasa.”

Ya mayar da rigar ga Imam Ali, kuma ya musulunta daga wannan rana.



Darasi daga wannan kissa:

Imam Ali ya koya mana gaskiya da bin doka – koda kai shugaban ƙasa ne.

Ya nuna cewa adalci ba ya bambanci tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba.

Halin Musulmi na kirki da gaskiya yana iya jawo mutane su karɓi Musulunci.

©️ Ya Hussain

Address

Aliyuibrahimmm33@gmail. Com
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Almajirin Sayyid Ibraheem Zakzaky posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category